Digital marketing na daya daga cikin digital skills da ake matukar samun kudi dashi a cikin wannan shekarar ta 2024.  Idan mutum yanaso yafara samun kudi da digital marketing skills yana da kyau ya bi wadannan hanyoyin 

Mutum ya fahimci mene digital Marketing 

A karon farko idan mutum yanaso yazama cikakken digital marketer yana da kyau ya fahimci me ma ake nufi da digital marketing sannan kuma me digital marketing ya kunsa. Yana da kyau mutum ya fahimci. 

  1. Hikimomin da suka shafi Digital marketing irinsu ilimin da ya shafi search Engine optimization (SEO), SEM (Search Engine Marketing), Content Marketing, Social Media Marketing Email Marketing, PP (Pay-per-click) da dai sauransu 

  2. Sannan Mutum yake karanta Blogs wato rubuce rubuce da suka shafi digital marketing irinsu Neil Patel, HubSpot, Moz da dai sauransu domin samun bayanai da suka shafi Digital marketing a ko da yaushe.  

Neman Ilimin da ya shafi Digital Marketing 

  • Dole ne mutum ya zage damtse wajen neman ilimin da ya shafi digital marketing akwai. manhajoji wato platforms da suke koyar da ilimin digital marketing a kyauta irinsu Coursera, Udemy, LinkedIn da dai sauransu. 

  • Sannan mutum yayi kokari yake registar courses da suke bayarda certificate a Companunuwa wanda suka sanu kamar irinsu Google da Hubspot

Neman Ilimin akan skills din dasu ke da alaka da Digital Marketing da kuma aiki da su 

Neman ilimi da kuma aiki da skills wanda suke da alaka da Digital marketing irinsu SEO da daisauransu 

  • Nafarko mutum ya fahimci abun da ake cewa SEO (search Engine Optimization) wato ilimin tura sakon talla ko kuma wani bayani a internet yaje in da akeso yaje 

  • Ya fahimci da kuma kwarewa akan sha’anin social media domin sanun dabarun tallata kaya ko kadara a kafafofin sadarwa na zamani irisu Facebook, Tiktok, LinkedIn da dai sauransu 

  • Yana da kyau mutum ya fahimci ilimin Email marketing wato yanda ake tallata kaya ta hanyar sakon Email. 

GINA portfolio 

Bayan neman ilimi da kuma kokarin aiwatar da ilimin da mutum ya koya na digital marketing ya na da kayau ya gina wa kansa portfolio wato ya samar da wasu ayyuka da ya taba yi ta yanda duk lokacin da aka tambayeshi experience dinsa akan digital marketing zai iya nuna su. Ana iya gina portfolio ne ta hanyoyi kamar haka 

  • Yin aiki na zahiri akan abun da ya shafi digital marketing wato mutum ya nemi wani aiki online wanda zayyi domin ya nuna kwarewarsa. Anan mutum zai iya fara neman voluntary job ko kuma internship domin ta nanne zai sami damar yin aiki akan abun da ya koya na digital marketing. Ana iya samun voluntery job ko kuma internship a LinkedIn da wasu manhajoji irinsa. 

KOKARIN NEMAN BAYANAI AKAN DIGITAL MARKETING AKO DA YAUSHE  

Ko da yaushe ana samun sababbin dabaru wanda zasu inganta harkokin digital marketing, dole mutum ya kasance yana kokarin neman ilimi akan sababbin dabaru da suka shafi digital marketing 

NETWORKING

Networking shine gina alaqa da mutanen da suke da ilimi ko kuma suke da ra’yin digital marketing, networking yana da matukar amfani a zamantakewar yanar gizo domin ta hanyar networking ne mutum zai ke samun sabbin bayanai da kuma damarmaki wanda suke da alaka da digital marketing 

MENTORSHIP. 

Mentorship yana da matukar amfani domin ta hanyar mentor ship ne mutum zai samu kwarewa sosai akan skills dinsa, mutum bazai ke kame kamen me yakamata yayi ko kuma ya aiwatarba yana da wanda zai ke tallafa masa da shawar wari akan dabarun aiwatar da aiki cikin kwarewa.